Connect with us

Labarai

A yau dokar hana kiwo da jihar Taraba ta kafa zai fara aiki

Published

on

A yau laraba ne dokar haramta kiwo da gwamnatin jihar Taraba ta kafa zata fara aiki, domin samar da zama lafiya a tsakanin manoma da makiyaya.

Gwamnatin jihar Taraba, daya daga cikin jihohin da suka kafa dokar hana kiwo a kasar nan.

Rahotanni dai sun bayyana cewa gwamnatin jihar tuni ma ta dauki zaratan jami’an hana kiwon da za’a yiwa lakabi da yan Marshal, kuma an dauko goma-goma daga matakan mazabun anguwanni wato wod-wod da suka kai dubu daya, inda za’a basu horo na musamman kafin bazasu a kananan hukumomin jihar goma sha shida.

Da yake karin haske ga manema labarai bayan wani taron sirri da sarakunan gargajiyan jihar, mataimakin Gwamnan jihar Taraban, Haruna Manu, yace dokar da zata soma aiki daga wannan rana ta 24 ga watan Janairu kuma ya samu amincewar sarakunan gargajiya, yayin da za’a soma aiwatarwa daki-daki.

Hon. Ibrahim Bappa Waziri tsohon jami’in tsaro ne kuma tsohon dan majalisar dokoki, yace kafin kafa irin wannan dokar akwai matakan da ya kamata a dauka. Kamar Bappa Waziri shima wani masanin Dokta Agoso Bamaiyi, yace ai wasu dokokin da ake fadi na burtali ko hurumin dabbobi, akwai bukatar duba su don tafiya

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!