Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Doke Real Madrid ya sanya muna fatan lashe La Liga-Xavi

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Xavi Hernandez, ya bayyana tawagarsa a shirye take na lashe gasar La Liga3 biyo bayan doke
Real Madrid da tai har gida da ci 4-0 a ranar Lahadi.

‘Yan wasa Pierre-Emerick Aubameyang da Ronald Araujo da kuma Ferran Torres ne suka zura kwallayen.

Wanda hakan ya sanya Barcelona doke Real Madrid a karon farko tin shekarar 2020.

Inda a gefe guda Real Madrid ta bawa Barcelona ta zarar maki 12 da wasanni 10 suka rage a kammala kakar wasannin shekarar da muke ciki.

Kafin fara aikin horar da tawagar da yayi Xavi, Barcelona na mataki na tara, wanda kawo yanzu ta koma mataki na uku bayan doke Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico.

“Matuka wasan da mukai ya zo da sabon salo, musamman yadda muka jajirce na ganin munyi nasara”

“Sai dai nasarar ta sanya muna yunkuri da kuma fatan lashe gasar ta La Liga da wasanni kadan ne suka rage a kamalla,” a cewar Xavi.

Bayan yunkurin lashe gasar da Barcelona dai keyi, na fatan kasancewa cikin kungiyoyin da zasu wakilci kasar Spain a gasar cin kofin zakarun turai a kakar wasanni mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!