Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dokin zuciya: Matashiya ta kashe ƙawarta a Kano

Published

on

Wata matashiya da ke unguwar Maidile anan Kano ta kashe ƙawarta ta hanyar yi mata yankan rago.

Lamarin dai ya faru ne bayan da rigima ta kaure a tsakaninsu a daren ranar Alhamis.

Tun da fari matashiyar da ta aikata kisan ta jife kawarta ta mai suna Bahijja da kalmar “Karuwa” inda ita kuma Bahijja ta mayar da martani.

Daga nan ne rikici ya kaure a tsakanin su, kuma nan take ƙawar ta ɗauko wuƙa bai Bahijja har gida tare da yi mata yankan Rago.

Sai dai ko da aka garzaya da Bahijja Asibiti don samun taimakon gaggawa tuni rai yayi halin sa.

Tuni rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wadda ake zargi tare aikewa da ita sashin binciken manyan laifuka, kamar yadda mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!