Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dole ne na maida da na makarantar ‘Yan Mari-Mahaifi

Published

on

Wani mahaifi mai suna Auwalu Umar Falgore yace shi dai ya kai dan sa ne makarantar Mari domin a kula mai da shi a kuma bashi tarbiyya sai dai kuma ya samu labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta  umarci da  a kule gidajen mari da suke fadi jihar kano.

Malam Auwalu ya ce ya wajaba ya maida dan na shi gidan Marin don yi masa tarbiyya.

Ya kara da cewa ya kai wannan yaron nashi gidan mari ne dalili kuwa bayajin magana kuma baya zuwa makaranta amma kuma sanadiyar  kaishi wannan gidan mari da yayi yasa yaron ya fara natsuwa.

Daga bisani dai mahaifin wannan yaro ya jawo hankalin gwamnati domin ganin cewa sun bullo da wani tsarin da zai maye gubin wannan gidan mari da suka sa aka kule.

Menene makomar ‘Yan Mari bayan da gwamnati ta soke ayyukan su.

‘Yan mari 36 sun shaki iskar ‘yanci a Kano

Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari

Daga bangaren kuma shi yaron da aka ce za’a mai yar da shi  yayi nadamar abunda yasa a ka kaishi gidan Mari kuma yayi fatan cewa bai zai kara ba, ya kuma yi kira da sauran yara masu irin wannan hali da su gyara domin kuwa ba shi da amfani .

Malamai dai da masu ruwa da tsaki tuni suka tofa albarkacin bakin su akan wannan al’amari na rufe gidan marin inda suke nuna cewa rufe gidan mari ka iya jawo matsala babba ga jihar kano domin haka gwamanti ta sanya idanu ta kuma kawo mafiyata ga al’amarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!