Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yarinyar da mahifinta ya garkame ta kamu da tabin hankali

Published

on

Wani mahaifi a karamar hukumar Madobi da ke cikin jihar kano mai suna malam Ujudu ya kulle “yar shi da ake kira da Binta a cikin daki har na tsahon sama da shekara uku, bincike ya tabbatar da cewa wannan yarinyar ta kamu da cutar tabin hankali sanadiyar wannan kule da mahaifinta yayi mata har na tsohon shekara 3 da “yan kai.

Bincike ya nuna cewa wannan yarinya bata fita daga cikin dakin da aka kulle ta hasali ma a nan take ci ta sha ta kuma yi bayan gida ta kwanta duk a wuri daya.

Wannan yarinyar dai ta samu kubuta ne daga daurin da mahaifin ta yayi mata ta dalilin hukamar NAPTIP da suka shiga suka fita dan gani cewa wa wannan yarinya ta kubuta daga wannan dauri da mahaifinta yayi mata.

Mahaifiya ta hallaka jaririnta a Kano

An gurfanar da uba da ‘yarsa gaban kotu bisa zargin shirya auren bogi

Mahaifiya ta hallaka jaririnta a Kano

Tuni da hukumar  NAPTIP  ta mika wannan yarinya izuwa hannun  ma’aikatar mata da walwala na jihar kano domin samun kulawa a hannun su.

Daraktan hukumar NAPTIP Shehu umar ya bayyana wa ma nema labarai cewa bawai sun cire hannun su bane a  wannnan al’amari ba  ya kuma kara da cewa suna kira da babbar murya wajen cewa an bawa wannan yarinya kulawar day a kamata.

Hajiya Binta Nuraini darakta mai kula da ofishin kananan yara a ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Kano tace za suyi iya kokarin su domin ganin cewa su baiwa wannan yarinya irin kulawar da ya dace kamar su, ci da sha da kuma suttura hadi da kuma kaita asibiti lokaci zuwa lokacin domin magance cututtukan da ke tare da ita.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!