Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

DSS: Ba mu muka azabtar da direban Shugaba Buhari har ya mutu ba

Published

on

Hukumar tsaron sirri ta Najeriya (DSS) ta musanta cewa ita ce ta azabtar da direban shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sa’idu Afaka wanda sanadiyar hakan ya rasa ransa.

DSS ta bayyana rahoton da ya alakanta ta da sanadiyar mutuwar direban shugaban kasar da jaridar ‘Sahara Reporters’ ta yada da cewa shifcin gizo ne kawai.

Tun farko dai jaridar ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa Sa’idu Afaka ya yaudari shugaban kasa wajen sanya shi ya sanya hannu kan wani kwantiragi wanda daga bisani aka gano cewa akwai almundahana cikin kwangilar

Wanda sanadiyar haka jami’an hukumar tsaron sirri ta DSS suka kama shi tare da azabtar da shi, bayan hakan ne kuma rai ya yi halinsa a asibitin fadar shugaban kasa.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ta DSS Dr. Peter Afunanya ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun sa, ya ce, hukumar DSS ba ta taba kama direban shugaban kasa ba ballantana har ta azabtar da shi, saboda haka ya bukaci al’ummar kasar nan da su yi watsi da batun.

‘‘Wannan labari ne marar tushe da bashi da makama’’ a cewar Afunanya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!