Connect with us

Labarai

DSS: Muna neman Sunday Igboho ruwa a jallo

Published

on

Hukumar tsaron sirri ta DSS ta bayyana jagoran tsagerun yarbawa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo.

 

Hukumar ta DSS ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a jiya alhamis.

 

Ta kuma ce jami’anta ne suka kai sumame gidan ɗan ta’addar da ke birnin Badun, wanda kuma tuni suka kashe biyu daga cikin jama’arsa, tare da kama wasu da dama.

 

Yayin taron manema labaran a shalkwatar hukumar ta DSS a Abuja, mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya, ya ce, duk wanda ya san inda Sunday Igboho ya ke, ya gaggauta sanar da hukumar, akwai tukuici mai yawa da za a bashi.

 

A cewar mai magana da yawun hukumar ta DSS, yayin sumamen, jami’an hukumar sun kama tarin makamai da kayan tsubbu a gidan jagoran tsagerun da ke ikirarin neman kafa ƴan tacciyar ƙasar Oduduwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!