Labarai
Wani dan jarida ya shiga tasku a hannun DSS
Jamian tsaro na DSS dake tsaron mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo sun daki wani danjarida dake aiki a fadar ta shugaban kasa wanda ke daukar hoto.
Danjaridar mai suna Abayomi Adeshida yace abun ya afku ne lokacin da mataimakin shugaban kasar ke duba wasu abubuwa da aka yi bajakolin su a taron da hukumar kula da harkokin kasashen waje ta shirya wanda aka gudanar a babban dakin taro na fadar shugaban kasa.
Danjaridar Abayomi Adeshida yace lamarin ya afku ne lokacin da yake daukar hoton mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo lokacin da yake zagawa a lokacin taron domin ganin kayan da aka yi baja kolin su.
Cibiyar CISLAC ta bayyana damuwar ta kan kamun da ‘yan sandan SARS ke yiwa ‘yan jarida
Wakilin Jaridar Thisday Ya tsallake rijiya da baya
Kungiyar NPO ta amince da sabon kudirin dokar aikin Jarida
Yace bai an kara ba sai ga wasu jamian tsaro na DSS su biyar sun yi masa tsawa sai kuma yaji ana dukan sa tare da jansa a kasa wanda haka ya sa suka lalata masa naurar da yake daukar hoto.
Yace dogarin mataimakin shugaban kasar ne ya kawo masa dauki .
Yayin da aka tuntubi mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu akande yace bai san lamarin ya faru ba amma yayi alakwarin zai bincika.