Labarai
DSS na tauye mini hakki na samun adalci – Abubakar Malami

Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da wasu ayyuka da ya ce suna da nufin tauye masa haƙƙinsa na samun adalci a shari’ar da ake yi masa.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka ya sanya wa hannu, Malami ya ce ana ci gaba da hana shi ganawa da lauyoyinsa lamarin da ke kawo masa cikas wurin kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa
Ya bayyana abin da hukumar ta DSS ke yi a matsayin wani mataki na yi wa doka zagon ƙasa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kama shi da aka yi ya zo ne a daidai lokacin da ya ke buƙatar ya kare kansa a shari’arsa da hukumar EFCC gaban babbar kotun tarayya.
Malami ya ƙara jaddada aniyarsa na kare kansa a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login