Labarai
DSS ta ceto sakataren karamar hukuma a Kano bayan sace shi

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa jami’an sun yi nasarar ceto sakataren gudanarwa na karamar hukumar Kibiya, Alhaji Hamza Durya, bayan kwanaki da aka sace shi.
Rahotanni sun ce an sace shi ne a daren Juma’a a gidansa da ke kauyen Durya cikin karamar hukumar Kibiya, inda wasu mahara dauke da makamai, kimanin mutum shida, suka iso kan babura suka tafi da shi ba tare da sun harbe kowa ba.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Waiya ya fitar, ya ce jami’an tsaro sun gudanar da aiki na hadin gwiwa wanda ya kai ga ceto mutumin tare da kama mutane biyu da ake zargi, inda aka ce sun samu raunukan harbi yayin aikin.
Gwamnatin ta yaba da kokarin jami’an tsaro, tana mai cewa hakan na nuna yadda dabarun tsaro ke aiki a fadin kananan hukumomi 44 na jihar, tare da jaddada kudirin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login