Connect with us

Labarai

DSS Ta gargadi ‘Yan Sanda kan yiwuwar sabon hari a Kwara da Neja

Published

on

Hukumar Tsaron farin kaya ta  DSS ta yi  da gargadin tsaro ga rundunar ‘yan sandan jihar Kwara  kan yiwuwar kai  wani sabon hari a kauyen Gbabe da ke karamar hukumar Baruten. 

 

Gargadin dai na zuwa ne   kwanaki kadan bayan mummunan harin da aka kai a kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama, inda aka kashe mutane da dama tare da tilasta wa wasu tserewa.

 

Hakan na cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Daraktan DSS na jihar ta Kwara  J.S. Adams, mai dauke da kwanan watan 5 ga Fabrairun 2026.

 

Sanarwar ta yi karin haske kan   taruwar wasu gungun mutane  dauke da makamai da ake zargin ‘yan kungiyar Mamuda ne a kusa da Kiyoru, gundumar Gwanara, da  ta ce akwai yiwuwar  su kai hari kan al’ummar Gbabe, tare da jaddada bukatar kara tsaurara matakan tsaro domin kauce wa tabarbarewar doka da oda. 

 

Hukumar ta kuma tunatar da tarihin ayyukan ta’addanci da kungiyoyin makamai ke yi a yankin Kainji, tare da bukatar jami’an tsaro su dauki matakan kariya cikin gaggawa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!