Kiwon Lafiya
Duk da farfadowa da tattalin arzikin Najeriya ke yi cikin sauri amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba-IMF
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce duk da farfadowa da tattalin arzikin Najeriya ke yi cikin sauri amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba sakamakon talauci da ke ci gaba da addabar al’ummar kasar nan.
Asusun na IMF ya kuma bukaci mahukuntan kasar nan da su bullo da wasu sabbin sauye-sauyen tattalin arziki cikin gaggawa domin shawo kan matsalar da ke neman gagaran Kundila.
Hakan na cikin wani rahoto ne na faifan Video wanda da asusun na IMF ya fitar akan tattalin arzikin kasar nan a jiya.
Rahoton asusun ya kuma ce akwai bukatar amfani da tsarin tattalin arziki na gajeren zango wanda za a ga alfanunsa nan take maimakon tsarin da zai dau tsawon lokaci.
Asusun na IMF ya ce akwai damuwa matuka ganin yadda kasar nan ke tunkarar babban zaben kasa a shekara mai zuwa a lokaci guda kuma da yakamata a ce hankalin gwamnati ya karkata wajen bullo da sabbin sauye-sauyen tattalin arziki.