Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Duk da kuɗin fansa: An gano gawar Hanifa bayan an yi garkuwa da ita

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta samu nasarar kama wani malamin makaranta da ake zargi da sace wata yarinyar nan mai suna Hanifa ƴar shekara biyar.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio.

Ya ce, an samu nasarar kama mutumin wanda kuma ake kyautata zaton malamin makarantar su Hanifa ne mai suna Abdulmalik Muhammad Tanko ɗan shekara 30 lokacin da yake ƙoƙarin karbar kuɗin fansar da suka nema domin sakinta.

Kiyawa ya kuma ce, ya tabbatar da cewa Hanifa Abubakar dalibarsa ce kuma ya sace ta ne a ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2021 inda ya kaita gidansa tare da abokinsa Hashim Isyaku dan shekara 37 wanda anan ne suka ɓoye ta tsawon sati biyu a Unguwar Tudun Murtala a Kano.

Yayin da daga baya suka haɗa baki da wasu mutane wajen hallaka ta duk da cewa sun karbi kuɗin fansa Naira miliyan 6.

DSP Kiyawa ya ce, da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!