Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun rufe makarantar da aka samu gawar Hanifa – Kwamishinan ilimi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantar Nobel Kids wadda marigayiya Hanifa ke yi, yarinyar da masu garkuwa da mutane suka sace tare da kashe ta anan Kano.

Kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Kiri ne ya bada umarnin rufe makarantar da yammacin ranar Alhamis.

“Mun samu labarin yin garkuwa da yarinya Hanifa a Kano tare da kashe ta, wannan labari ya girgiza kuma hakan ya nuna akwai buƙatar ayi bincike mai ƙarfi akan irin waɗannan makarantu” a cewar Ƙiru.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa “Don haka mun rufe makarantar daga yau Alhamis har sai abinda bincike yayi, don haka iyaye su janye yaransu daga makarantar kuma za mu zuba jami’an tsaro don tabbatar da ba a bude makarantar ba”.

Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ya ce, makarantar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an kammala bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!