Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dukkan wanda za’a nada a kunshin sabuwar gwamnati sai ya bayyana kadarorinsa

Published

on

Sabon zababben gwamnan jihar Kano Engineer Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin cewa, dukkan wanda za’a nada a kunshin gwamnatin sa ya zama wajibi ya bayyana kadarorin sa, kafin a bashi mukami.

Sakataren yada labaran zababbiyar gwamnatin ta jihar Kano Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aiko wa Freedom Radio a daren jiya Juma’a.

Ta cikin sakon Dawakin Tofa yace sabon zababben Gwamnan ya yi haka ne domin tabbatar da an yi biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar nan, da yai umarnin cewa duk wanda za’a nada wani mukamin gwamnati ya zama wajibi ya bayyana kadarorin sa.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!