Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Anci tarar mutane 57 da suka karya doka yayin zagayen tsaftar muhalli a kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce yayin zagayen tsaftar muhallin na yau Asabar, inda jimullar mutanen da suka karya doka sun kai 57, yayin da kuma adadin kudin tarar da aka samu ya kai dubu talatin da biyar da dari daya.

Babban sakataren ma’aikatar muhalli Aliyu Yakubu Garo ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala duban tsaftar muhalli na karshen wata a yau.

Sai dai kuma Aliyu Garo duk da haka ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa biyayya ga dokar tsaftar muhalli da suka nuna.

Wanda ya ‘ce a wuraren da suka je daya kai sama da goma da suka hadar da kasuwanni da tasoshi, inda suka gannewa idanun su yadda mutane suka jajirce wajen ganin sun tsabtace muhallansu’.

Freedom Radio ta rawaito cewa an samu ci gaba a fannin tsaftar muhalli musamman yadda jama’a suke ba da hadin kai a lokacin aikin.

Rahoton: Madina Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!