Kasuwanci
E-Naira zai farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce amincewa da tsarin hada-hadar kuɗaɗ€n internaet na eNaira da babban Bankin ƙasa CBN ya fito da shi zai taimawa wajen bunƙata tattalin arziƙin ƙasa.
Shugaban buhari ya bayyana hakan a lokacin da yake ƙaddamar da tsarin na eNaira a ranar Litinin a Abuja.
Ya ce, tsarin zai bunƙasa tattalin arziƙi zuwa dala biliyan 29 a cikin shekaru 10 masu zuwa.
Ya ce, ta hanyar ƙaddamar da tsarin eNaira, Najeriya ta zama ƙasa ta farko a Afirka, kuma daya daga cikin na farko a duniya da ta ƙaddamar da shi.
Shugaban ya ce akwai fa’idodin musamman na Najeriya na kudin dijital wanda ya ratsa sassa daban-daban na tattalin arziki.
“A cikin lokutan baya-bayan nan, yin amfani da tsabar kuɗi wajen gudanar da kasuwanci na raguwa; wannan yanayin ya taɓarɓare ta hanyar bullar cutar ta COVID-19 don hawa wannan tsari zai farfaɗ sake farfado da sabon Tattalin Arziki na zamani.
A cewar shugaban, kasashe kalilan da suka hada da China, Bahamas, da Cambodia sun riga sun fara wannan tsari na eNaira.
You must be logged in to post a comment Login