Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abubuwa 8 da Buhari ya fada cikin sakon sabuwar shekara

Published

on

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi wa  al’ummar Najeriya jawabin shigowa sabuwar shekara da misalin karfe bakwai na safiyar yau Juma’a bayan da aka shiga daya ga watan junairun shekara ta 2021.

Abubuwa da Shugaban kasa ya fada cikin sakon sa na sabuwar shekara.

Muhammad Buhari ya fara gabatar da jawabin ne na kai tsaye ta gidan talabijin na kasa NTA ya watsa da safiyar yau.

Muhammadu Buhari ya tabo batutuwa da dama mussaman ma wanda zai ciyar da kasar nan gaba, daga ciki akwai

Daga cikin wajabin na shugaban kasar ya fara godewa Allah kan irin abubuwan da aka gani a shekara ta 2020.

Muhammadu Buhari  a ya yin jawabin nasa mai tsawon minti 18 da dakika 56 ya bayyana cewa a ‘yan  Najeriya sun fuskanci matsi da wahalhalu kasancewar annubar cutar Corona ta yi tasiri a duniya, a don haka tattalin arzikin duniya ya shiga wani wadi ciki har da Najeriya.

Shugaban kasar ya kuma yayi jawabi matsalar tsaro da da ya addabi kasar nan.

‘Yan Najeriya su ci gaba da hakuri shekarar 2021 zata zo da sauyi

Gwamnatin Najeriya ta ce shekarar 2021 za ta zowa al’ummar kasar da sauye sauye ta fannnin sha’anin tsaro da tattalin arziki da al’amuran more rayuwa.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ne ya bayyana hakan a jawabin da yayiwa al’ummar kasar na shiga sabuwar shekara ta 2021 da safiyar ranar Juma’a.

Annobar Corona

Muhammad Buhari ta cikin jawabin nasa ya ce shekarar 2020 ta zowa al’ummar kasar da matsaloli da suka shafi bullar Annobar cutar Corona wanda ya kasara tattalin arzikin kasar nan.

Matsalar tsaro

Ta cikin jawabin nasa Muhammad Buhari ya ce Najeriya ta fuskanci farmakin ‘yan ta’adda da garkuwa da mutane a sassan kasar nan musamman ma yankin Arewa.

Yana mai jinjinawa jami’an tsaron kasar bisa nasarar da suka samu na kwato ‘yan makarantar sakandaren Kankara da masu garkuwa suka sace su a watan Disambar shekarar ta 2020.

Ayyukan raya kasa

Ya kuma ce a domin haka gwamnatin sa  zata ci gaba da yiwa al’ummar Najeriya ayyukan raya kasa tare da kula da lafiyar su da dukiyoyin su a shekarar da aka shiga ta 202.

Gwamnati zata mayar da hankali wajen samarwa matasa aikin yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, a shekarar 2021 gwamnatinsa zata mayar da ahanakali wajen samarwa matasan kasar ayyukan yi don samar musu da kyakyawar makoma a nan gaba.

Shugaban ya ce, za suyi hadin gwiwa da hukumomin kasar nan wajen samar da tsarin da zai dora matasan kasar kan ayyukan yi don magance matsalar zaman banza da ke kara haddasa ayyaukan ta’addanci.

Yaki da cin hanci da rashawa.

Da yake batu kan ayyukan cin haci da rashawa shugaba Buhari ya ce, gwamnatin sa zata mayar da hanakali a wannan shekarar don ganin ta kawo karshen ayyukan cin hanci da rashawa musamman tsakanain hukumomin kasar nan.

Yaki da Talauci.

Ko da shugaban ke batu kan talauci, ya ce matakin samarwar matasana ayyukan yi zai taimaka wajen farfadowar tattalin arziki tare kawar da tunanin ga barin shiga ayyukan ta’addanci.

Farfado da tattalin arziki.

Daga cikin abinda shugaban ya bayyana a sakon sabuwar shekara sun hada cewa Gwamnatin sa zata mayar da hankali wajen farfado da tattalin arziki tun daga tushe ta hanyar watada kasar nan da abinci.

Yana mai cewa gwamnatin sa  zata bunkasa  tattalin arziki Najeriya  wajen baza komar sa a rage dogaro akan man fetur.

Buhari ya ce wannan yunkuri zai  taimaka wajen tada komadar tattalin arziki ganin yadda yanayin da kasar nan ta tsinci kanta  a ciki musamman  a lokacin Corona  da aka yi kulle kuma gashi ya sake dawowa a karo na biyu.

Jawabin nasa dai na zuwa cikin sakon taya muranar sabuwar shekara ga al’umma kasa da ya gudanar a safiyar yau.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!