Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

EDO 2020: Akwai yiwuwar sauya mai masaukin baki – MYSD

Published

on

Ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa ta fara yunkurin amfani da Abuja a matsayin mai masaukin baki a gasar bikin kakar wasanni ta 2020.

Tunda da fari dai anyi niyyar gudanar da gasar ne da akayi ta dagewa sakamakon bullar cutar Corona da kuma matsalar karancin kudade a jihar Edo.

Za a fara gasar a ranar 2 ga watan Afirilu kuma a karkare ranar 14 ga watan na Afirilun 2021.

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce, ya rubuta wa gwamnatin tarayya takarda don ta baiwa jihar Edo tallafin kudi da zata alkinta wajen gudanar da gasar yayin da jihar ke kokawa kan matsalar karanci kudi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wani mutun a ma’aikatar wasannin ta kasa wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, ma’aikatar ta fara yunkurin maye gurbin jihar ta Edo da Abuja a matsayin inda za a gudanar da gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!