Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nijar: An kama sojojin da su ka yi yunkurin juyin mulki

Published

on

Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kama wasu sojoji a Jamhuriyar Nijar biyo bayan yunƙurin juyin mulkin da wasu dakaru suka yi a daren Laraba.

Har yanzu babu cikakken bayani game da abin da ya faru yayin da birnin Yamai ya kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

Tun misalin ƙarfe 3:00 na dare aka fara jin harbe-harben kuma an ɗauki tsawon kusan minti 15 ana yi.

Jami’an tsaron fadar shugaban ƙasa ne suka daƙile yunƙurin, wanda ya faru ƙasa da kwana biyu kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum.

(BBC)

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!