Labarai
EFCC ta bankado badakalar Naira Biliyan 70 a harkar tallafin man fetur
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) Abdurrasheed Bawa, ya ce, hukumar ta bankado wata badakala a harkar tallafin man fetur da ta kai naira biliyan saba’in.
Ya ce naira biliyan ashirin ne kacal cikin kudaden gwamnati ta samu nasarar kwato su.
Abdurrasheed Bawa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a harabar babbar kotun jihar Lagos da ke Ikeja.
Rahotanni sun ce Abdurrasheed Bawa ya gurfana gaban kotun ne don ba da shaida kan wata shari’a da ake yi kan badakalar tallafin man fetur da ya shafi wani kamfani mai suna Nalado Energy wanda ya kai naira biliyan daya da miliyan dari hudu.
Shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana damuwarsa matuka kan yadda ya ce shari’un zargin badakalar tallafin man fetur ke tafiyar hawainiya.
‘‘Yanzu haka muna kokari ne wajen ganin mun kama wani mutum da ake zargi da hannu a badakalar tallafin man fetur wanda aka taba kamashi a shekarar 2012, amma bayan an ba da belinsa ya tsere ya bar kasar nan’’, a cewar Bawa.
You must be logged in to post a comment Login