Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Duk wanda ya mutu bayan karbar allurar rigakafin Corona ajalinsa ne ya cika – El-Rufa’i

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ce babu abinda ya same shi bayan da aka yi masa allurar rigakafin cutar Covid-19, a don haka jama’a ku daina jin tsoro.

“Bayan an yi min allurar an bukaci da in zauna tsawon mintina 15, kuma na zauna har minti 20 sannan na tashi, ban ji wani abu ba, babu ciwon kai ba wani abu, yanzu haka ma mota zanshiga in tafi Abuja”, inji Gwamnan.

“Gwamnatin kasar Saudi Arebiya ta ce babu wanda zai je aikin Hajjin bana sai yana da shaidar karbar allurar rigakafin, kuma ba ta da wani lahani.”

“Mu ba mu ji labarin ko allurar ta taba zama silar mutuwar wani ba, idan wa’adin mutum ya cika to babu makawa sai ya tafi, amma dai ba allurar ce ta kashe shi ba”, a cewar El-Rufa’i.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!