Labarai
EFCC ta tsare tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta tsare tsohon Ministan Shari’ar kasar nan , Abubakar Malami, saboda gaza cika sharuddan Beli da aka ba shi, inda ya ci gaba da zama a tsare har zuwa daren Jiya Talata.
Hukumar ta bayyana cewa tana binciken sa bisa zargin almundahanar kuɗi, bude asusun Banki na Bogi,da ba’a gama tantance mai su ba da kuma zargin daukar nauyin ayyukan ta’addanci, ciki har da batun kudaden Marigayi Janar Sani Abacha da wasu kudade daga ƙasashen ketare.
EFCC ta ce ana binciken sa kan laifuka 18, kuma har yanzu ba a iya tantance adadin kudin ba tukunna, yayin da Malami ya musanta zarge-zargen yana cewa dukkan su kirkirarru ne.EFCC ta tsare tsohon Ministan Shari’ar kasar nan , Abubakar Malami, saboda gaza cika sharuddan Beli da aka ba shi, inda ya ci gaba da zama a tsare har zuwa daren Jiya Talata.
Hukumar ta bayyana cewa tana binciken sa bisa zargin almundahanar kuɗi, bude asusun Banki na Bogi,da ba’a gama tantance mai su ba da kuma zargin daukar nauyin ayyukan ta’addanci, ciki har da batun kudaden Marigayi Janar Sani Abacha da wasu kudade daga ƙasashen ketare.
EFCC ta ce ana binciken sa kan laifuka 18, kuma har yanzu ba a iya tantance adadin kudin ba tukunna, yayin da Malami ya musanta zarge-zargen yana cewa dukkan su kirkirarru ne.
You must be logged in to post a comment Login