Labarai
EFCC:ta ja hankalin Bukola Saraki da ya san yarda zai kare kansa
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ta shawarci tsohon shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da cewa, gara ya je ya san yadda zai kare kansa gaban kotu, maimakon ci gaba da bata sunan mai rikon mukamin shugaban Hukumar Ibrahim Magu.
A cewar Hukumar ta EFCC, ci gaba da bata sunan Ibrahim Magu da Sanata Bukola Saraki ke yi, ba zai canja komai ba, game da shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi gare shi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin jami’in yada labaran Hukumar Mr. Tony Orilade.
Sanarwar ta ce, a baya-bayan nan Sanata Bukola Saraki wanda yanzu haka ba ya kasar nan, ya dauki gabarin amfani da kafafen yada labarai, wajen cin zarafi tare da bata sunan mai rikon mukamin shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, sakamakon gurfanar da shi game da zargin cin hanci da rashawa.
A cewar sanarwar, abin takaici ne sai da Sanata Bukola Saraki ya bar kasar nan sannan ne zai fara yada farfaganda akan Hukumar EFCC.
A don haka ta cikin sanarwar Hukumar EFCC ta ce, babu gudu ba ja da baya game da ci gaba da gurfanar da Sanata Bukola Saraki da sauran mutanen da ake zargin su da laifuka na cin hanci da rashawa a kasar nan.
Hukumar EFCC ta cikin sanarwar ta ma buga misali da wani rahoto da aka wallafa a jaridar ‘Punch’ wanda shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki ya shaidawa mai shari’a Abdul Kafarati cewa, mai rikon mukamin shugaban Hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ya taba rokon sa cewa, da ya taimaka mishi domin majalisar dattawa ta amince da shi a matsayin shugaban EFCC da cewa abin dariya ne.