Labarai
EHealth Academy ta yaye matasa 100 da ta horas kan harkokin Fasahar zamani

Ƙungiyar E Health mai zaman kanta, ta yaye ɗalibai ɗari da ta koya wa ilimin harkokin fasahar zamani a kyauta ƙarƙashin makarantarta ta E Health Academy domin ƙara bunƙasa fasahar Sadarwar zamani da kuma inganta fannin.
Babban jami’i a ƙungiyar Malam Jamil Aliyu Galadanci, ne ya bayyana hakan a yau Juma’a yayin bikin yaye ɗaliban wanda makarantar ta gudanar a nan Kano.
Malam Jamil Aliyu Galadanci, ya ce, kimanin ɗalibai 2,000 ne suka nemi shiga cikin shirin, inda 200 daga ciki suka yi nasarar samun gurbin tallafin karatu, amma 100 daga ciki ne suka samu nasarar kammalawa sakamakon yadda sauran suka gaza ƙarasa karatun.
” Muna koyar da wadannan matasa ne domin su kasance kwararru musamman a fannin harkokin Kwamfuta da kuma sauran harkokin fasaha, inda yanzu haka dukkansu kwararru ne, inji Jamil Aliyu Galadanci.”
Haka kuma ya kara da cewa, za su ci gaba da daukar irin wadannan matasa domin su ma su ci gajiyar irin wannan tallafi na horas da du harkokin fasaha.
ya kuma ce, akwai matasa da dama daga cikin wadanda kungiyar ta koya wa irin wadannan fasahohi da suke yin aikin sa kai a cikinta, inda yanzu haka sun mayar da wasu daga ciki zuwa cikakkun ma’aikata da suke biyansu albashi.
A nasa ɓangaren, kwamishinan ma’aikatar Kimiyya da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire ta Kano Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren ma’aikatar Malam Abba Adamu Dan-guguwa, ya yaba da irin gudunmawar da E Health Academy ke bayarwa musamman ma ga matasa inda kuma ya bukaci ɗaliban da aka yaye da su yi amfani da abinda suka koya wajen bunƙasa harkokin Kimiyya da fasaha tare da kawo sabbin ababen ci gaba ga al’umma.
You must be logged in to post a comment Login