Labarai
Za mu wajabta amfani da fasahar AI- Jami’ar Bayero

Jami’ar Bayero da ke Kano ta sha alwashin fito da tsare-tsaren da suka yi dai-dai da zamani wajen amfani da fasahar zamani ta AI, wajen koyarwa a tsangayar ilimi da ke jami’ar domin samar da sauki a fannin karatun dalibai.
Shugaban tsangayar ilimin farfesa Abubakar Ibrahim Hassan, ne ya bayyana hakan a yau yayin cikar tsanyar shekaru 50 da kafuwa inda ta yaye manyan mutane da dama a ƙasar nan.
Farfesa Abubakar Ibrahim Hassan, ya ƙara da cewa ya zama wajibi duk sassan koyarwa su rika yin amfani da fasahar ta AI, domin samun sauki a fannin koyarwa.
Da ta ke jawabi, ƙaramar ministar ilimi Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce, shirya wannan taro abu ne mai muhimmanci musamman yadda tsangayar ta yaye manyan mutane.
Ministar ta kuma ce, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da duk wata gudunmawa ga jami’ar domin ƙara inganta ta domin ta ci gaba da riƙe kanbunta na ya ye dalibai haziƙai.
You must be logged in to post a comment Login