Connect with us

Kaduna

El-rufa’I ya kayyadewa masu adai-daita sahu wuraren zirga-zirga a Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce daga ranar litinin mai zuwa ne dokar da gwamnatin jihar ta sanya ta hana amfani da baburan adai-daita sahu bin wasu manyan hanyoyin jihar za ta fara aiki.

Shugaban hukumar kula da harkokin sufuri ta jihar Kaduna Malam Lawal Musa Usman ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.

“Dokar zata dakatar dasu su rika aiki a manyan hanyoyi kamar, Ali Akilu Road, Ahmadu Bello Way da kuma Western by Pass da wuraren Unguwar Rimi” a cewar sa.

Wakilin Freedom Radio Kaduna, Aliyu Abdullahi Jama’are ya rawaito Lawal Musa na cewa ce anyi hakan ne domin dakile yawaitar afkuwar hadura a manyan titunan jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!