Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

El-Rufai zai fara raba magunguna ta hanyar amfani da jirage masu sarrafa kan su

Published

on

Gwamna Nasir El-Rufai  ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani, a wani  mataki na raba magunguna  a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya  na jihar Kaduna ta hanyar amfani da kananan jirage masu sarrafa kawunansu (drones) wanda aka yi yau.

A jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya ce wannan kamfani  da ke Kasar Amurka wanda ke da reshe a Kasar Ghana ya zabi Jihar Kaduna ne don ganin yadda jihar ta dauki sha’anin kiwon lafiya da muhimmanci.

Gwamnan ya kara da cewa, “ wannan tsari zai taimaka mana wurin rarraba magani da alluran riga-kafi zuwa duk lunguna da sakunan da ke jihar nan musamman inda muke fama da matsalolin tsaro kamar Birnin Gwari.

Sannan wannan tsarin zai taimaka mana wurin samar da ayyukan yi ga matasanmu tun da a nan Kaduna za su rika kera wadannan jirage masu sarrafa kawunansu”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!