Labarai
EU tace bata da masaniya kan cewa INEC nada rumbun adana bayanai
Wakilan Kungiyar tarayyar Turai da su ka sanya idanu kan yadda zaben Najeriya ya gudana sun ce basu da wata masaniya game da mallakar rumbun adana bayanai na Hukumar zabe ta Najiya INEC.
Rahoton kungiyar ta EU ya yi kafar Ungulu da ikirarin da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar su ka yi na cewa Hukumar zabe ta Najeriya INEC tana da rumbun adana bayanai.
Hakan na cikin wani rahoto da wakilan kungiyar ta tarayyar Turai su ka gabatar jiya a Abuja, game da manyan zabukan Najeriya da suka gudana a wannan shekara.
Da ta ke karanta sakamakon rahoton babbar jami’ar Hukumar tarayyar Turai da ta jagoranci sanya idanu kan zabukan, Hannah Roberts, ta ce, basusan da wani rumbun adana bayanai kamar yadda labarin ke yaduwa a kasar nan.
Tun farko dai jam’iyyar PDP da dan takaranta Atiku Abubakar sun yi ikirarin cewa Hukumar zabe ta kasa INEC ta yi amfani da rumbunta na adana bayanai wajen aikawa da kuma karbar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar ashirin da uku ga watan Fabrairun bana.