Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

EXPO 2020: Buhari zai tafi haɗaɗɗiyar daular Larabawa

Published

on

A yau Laraba ne ake sa ran shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja domin halartar bikin EXPO 2020 a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

A ranar Asabar mai zuwa ne shugaba Buhari zai kasance babban bako na musamman a bikin mai taken: bude Damarar Zuba Jari a Najeriya.

Bikin baje kolin dai zai sake bai wa Najeriya damar bayyana gagarumin ci gaban da aka samu a fannin tattalin arziki a cikin shekaru shidan da suka gabata a matsayin ginshikin mayar da kasar muhimmiyar makoma ta zuba jari kai tsaye daga ketare.

Kazalika taron zai bai wa Najeriya damar shiga cikin ƙasashe sama da 190 don kulla alaka mai kyau da samar da makoma.

Shugaban Buhari zai samu rakiyar wasu daga cikin ministocin sa da suka haɗar da ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama da ministan masana’antu Ciniki da zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo da ta Kudi kasafin da tsare-tsare Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed.

Buhari na ganawa da shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa

Sai ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai ritaya da ministan jiragen Jirgin sama, Sanata Hadi Sirika da na Noma da Raya Karkara, Daka Mohammad Mahmud Abubakar.

Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Abuja a ranar Lahadi 5 ga Disamba, 2021 kamar yadda sanarwar da Femi Adesina mai mataimakawa shugaban kan harkokin yaɗa labarai ya fitar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!