Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Jama’ar Musulmi na alhinin rashin Malam Mas’ud Hotoro

Published

on

Al’ummar musulmi na jimamin rasuwar Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro ɗaya daga cikin Malaman da suka yi muƙabala da Malam Abduljabbar Kabara.

Bayanan da Freedom Radio ta tattara sun nuna cewa Malam Mas’ud Hotoro ya rasu a daren Talata a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Ɗaya daga cikin makusantansa kuma shugaban hukumar yaƙi da barace-barace ta jihar Kano Malam Albukhariy Mika’il ya tabbatarwa da Freedom Radio wannan rasuwa.

Mika’il ya ce, yanzu haka tuni suka isa garin Zariya domin ɗauko gawar mamacin.

“Su shida ne a motar huɗu daga ciki sun rasu, biyu kuma sun tsira yanzu haka suna asibiti”.

Ya ci gaba da cewa “Mun zo ofishin hukumar Road Safety sun bamu wayarsa da kuɗin da ke jikinsa, daga nan zamu wuce asibitin Shika sannan mu kamo hanya zuwa Kano”.

Yadda aka samu labarin rasuwar

Malam Albukhariy Mika’il ya ce, da tare za su tafi Kadunan, amma bai samu zuwa ba.

“Ya kirani da yamma cewa zai taho, daga nan kuma sai kiran wayata aka yi da wayarsa cewa ya rasu”.

“Tun cikin dare muke ta magana da jami’an hukumar kiyaye afkuwar haɗura, hakan ya sa muka kamo hanya tun da asuba”.

“Hukumar KAROTA ta bamu Ambulance da muka taho da ita domin ɗaukar gawarsa”.

Yaushe za a yi masa jana’iza
Malam Bukhariy ya ce, za a yiwa marigayin jana’iza da zarar sun iso da gawarsa zuwa Kano.

Marigayi Malam Mas’ud Hotoro shi ne ya wakilci ɗariƙar Ƙadiriyya a muƙabalar da aka yi da Abduljabbar Nasir Kabara.

Yanzu haka dai tuni al’umma suka shiga jimamin rashin marigayin .

Jama’a da dama na bayyana alhininsu na wannan rashi a kafafen sada zumunta.

Allah ya gafarta masa Amin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!