Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Eyitayo Jegede ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan Jihar Ondo

Published

on

Eyitayo Jegede mai lambar kwarewa ta SAN ya lashe zaben fidda gwani na takarar gwamna a Jihar Ondo, bayan doke abokan takararsa guda guda bakwai, ciki har da mataimakin gwamnan Jihar Agboola Ajayi, wanda ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP.

Eyitayo Jegede ya samu kuri’u 888, inda wanda ya yi ma sa na biyu kuma mataimakin gwamna Agboola Ajayi ya samu kuri’u 657.

Sauran sun hadar Eddy Olafeso da ya samu kuri’u 175, Bode Ayirinde da ya samu kuri’u 95, yayin da Banji Okunomo ya samu kuri’u 90.

Eyitayo Jegede shi ne dantakarar gwamna a jam’iyyar PDP a shekarar 2016, wanda ya sha kayi a hannun gwamna mai ci Rotimi Akeredolu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!