Connect with us

Manyan Labarai

Majalisar dinkin duniya ta yi Allah-wadai da harin ‘yan Boko Haram

Published

on

Majalisar dinkin duniya ta yi Alla-wadai da kisan ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi wa wasu ma’aikatan bayar da agaji guda biyar a jihar Borno, bayan kama su a Munguno cikin watan Yunin da ya gabata.

Wannan na cikin wata sanarwa da babban jami’in bayar da agaji na majalisar dinkin duniya a Najeriya Mr Edward Kallon ya fitar a jiya, yana mai nuna kaduwarsa da yadda ‘yan Boko Haram din suka hallaka ma’aikatan na su.

Edward Kallon ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da sauran ‘yan uwa da abokan aikinsu.

A jiya laraba ne dai kungiyar Boko Haram ta fitar faifan bidiyon yadda suka kashe ma’aikatan agajin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,091 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!