Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Fadar shugaban kasa ta ce rade-raden kin sanya isasun kudin ra’ayin wasu ne na cimma burinsu

Published

on

Fadar shugaban kasa ta bayyana rade-rade da kuma zargin da wasu ‘yan majalisar suke yi kan cewa majalisar zartarwa da gangan suka ki sanya isasun kudaden cikin kunshin kasafin kudin bara ake don cimma burin su na kanshin kan su.

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan al’amuran majalisar datijjai Snata Ita-Enang ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Ita-Enang ya dage kan cewa, ‘yan majalisar dokoki ta kasar nan na daya daga cikin matakan gwamnatocin kuma sun fi kowa karabar kudaden daga asusun gwamnatin tarayya cikin kunshin kasafin kudin bara.

Wasu daga cikin sanatoci da ‘yan majalisar wakilai dai cikin wata tattaunawa da manema labarai daba-daban suka ce mai yuwa ne a sami rikici tsakanin bangaran zartarwa da na ‘yan majalisar, in har shugaban kasa Muhammadu Buhari yaki amincewa da fitar da kudaden kunshin kasafin kudin shekara ta 2018 ga ‘yan majalisar dokoki ta kasa.

A dai kwanan baya ne ‘yan majalisar suka yi zargin cewa ‘yan majalisar zartarwa sun ki amincewa da fitar da kudin ga ‘yan majalisar wani mataki na basu horo saboda yadda ake yawan samun sabani a tsakanin bangarorin 2.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!