Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta biya ma’aikatan rusashen kamfanin jirgin saman Najeriya kudaden sallama

Published

on

Gwamantin tarayya ta fito da sunayen mutane 114 wadanda tsoffin ma’ikata rusashen kamfanin jirgin saman na kasa Nigerian airways ne, da aka biyasu kudaden sallama daga aka aiki har sau biyu, kuma suka ja bakin su suka yi shiru.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ma’aikatan harkokin sufirin jiragen sama ta kasa AUGA Lukuman Animashauna  ya fitar a jiya.

Ta cikin sanarwar kungiyar ta ce gwamnatin tarayya ta sanar da ita cewar ta lurta da an biya wasu ma’aikatan har sau biyu amma sun tsuke bakunan su sun yi shiru.

Sanarwar ta kuma bukaci dukkanin mutanen da aka yiwa aringizon, da su ziyarci bankunan su a yau Litinin domin gyara matsalolin nasu, ta yadda za a baiwa wadanda basu karba ba damar samun nasu kudaden.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewar duk wanda ya ki halartar bankin nasa domin gyara matsalar sa a yau litinin to ba shakka za a cire shi daga cikin wadanda za su ci ga ba da amfana dafanshon su baki daya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,749 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!