Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Buhari na nan kan bakansa na tsayawa takarar shugabanci

Published

on

Fadar shugaban kasa ta ce zance ne maras tushe  da wasu al’ummar kasar nan ke yadawa na cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai nemi takara a karo na biyu ba duba da yawan shekarun sa.

 

Mai magana da yawun shugaban kasar kan kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana haka da yammacin jiya Talata ta kafar talabijin ta Channels

 

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana kudurin sa na sake neman takara akaro na biyu jim kadan kafin tafiyar sa Birnin London

 

A cewar sa idan ma da wata magana mai kama da wannan to al’ummar kasar nan basu fahimci batun ba, inda ya ce, shugaban kasar a wani a wani lokaci a baya ya ce yana sha’awar ya shugaban ci kasar nan domin ya gyara matsalolin ta.

 

Sai dai kuma ya ce lokacin da shugaban kasar ya nemi takara a shekarar 2011 ya ce, idan ya ci zaben zai yi zango guda ne kawai, sai dai a cewar Adesina Buhari baici zabe a wannan shekarar ba, kuma a nan wannan magana ta kare.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!