Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Fadar shugaban kasa ta maida martani kan sauke manyan hafsoshi

Published

on

Fadar shugaban kasa ta ce it ace ke da alhakin sauke manyan hafsoshin kasar nan.

Wannan na kunshe ta cikin sanarwar da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafin ta na Twitter cewa, Muhammadu Buhari ne kadai ke da ikon nadawa tare da sauke manyan hafsoshin kasar nan.

Fadar shugaban kasa na maida martini kan bukatar da majalisar dattijai ta yin a sauke su daga kan mukaman su kan matasalar tsaro a kasar nan.

A dai dazu ne majalisar dattijai ta bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar nan da su sauka daga kan mukaminsu.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da shugaban kwamitin kula da rundunar sojojin kasar nan, Sanata Ali Ndume ne ya gabatar a yau.

Sanata Ali Ndume wanda shine sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar ta dattawa ya ce la’akari da halin da ake ciki na matsalolin tsaro wanda har ya kai wasu daga cikin sojoji na barin aiki lokacinsu bayyi ba, akwai bukatar shugabannin tsaron da su sauka daga mukaminsu.

Sanata Ali Ndume ya ce ci gaba da kasancewarsu akan harkokin tsaron kasar nan ba yi da wani tasiri kasancewar basu dakile matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!