Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Na shirya ficewa daga jam’iyyar PRP – Salihu Takai

Published

on

Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PRP Malam Salihu Sagir Takai ya ce yanzu haka ya shirya ficewa daga jam’iyyar ta PRP mai ‘dan mukulli.

Daraktan yakin neman zaben Malam Takai, wato Barista Faruk Iya Sambo shi ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio.

Iya Sambo ya ce, yanzu haka su na ci gaba da tattaunawa a tsakanin su domin cimma matsaya kan jam’iyyar da ya kamata su koma.

“Mun tattauna da jama’ar mu na kananan hukumomi 44, da kuma sauran wadanda suka taimaka mana a zabe, yanzu muna kan tsayar da matsaya, tsakanin jam’iyyu uku, PRP da muke ciki, ko kuma PDP da APC wadanda kowanne da mutanen mu a ciki” a cewar Faruk Iya.

Cikakken labarin zai zo muku a shirin mu na “Kowane Gauta” da karfe 9pm da kuma maimaici da karfe 7:30am.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!