Connect with us

Kiwon Lafiya

Farashin danyen man fetur ya daga a kasuwar Duniya

Published

on

Farashin danyen Man Fetur ya daga a kasuwar Duniya sakamakon tsammanin cewa kasar Amurka ka iya sake sabunta wani takunumin cinikayya kan kasar Iran mai arzikin Man Fetur.

An sayar da gangar man a jiya Litinin kan farashin Dala 65 da Centi 18 da ke nuni da cewa farashin ya karu da Centi digo hudu inda kuma aka yi cinikin Man da aka tace kan farashin Dala 69 da digo 67, da ke nuni d cewa farashinsa ya karu da digo 5.

Shugaban sashen kasuwanci da dillanci na wani kamfanin dillancin Man fetur din a kasar Singapore Stephen ya ce ‘yan kasuwar sun kasance cikin halin rashin tabbas sakamakon tsoron shin ko Amurkar za ta ci gaba da wata yarjejeniyar Nuclear da kasar Iran ko a a.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!