Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin tarayya ta kara farashin man fetur

Published

on

Hukumar kayyade farashin man fetur ta Najeriya ta sanar da cewa an kara farashin man daga naira 140.80 zuwa 143.80 kan kowacce lita.

Wata sanarwa mai dauke da kwanan wata daya ga watan Yuli da hukumar ta aikewa dillalan man fetur, ta ce bayan sake nazarin jadawalin farashi da aka yi na watan Yuni, an yi la’akari da yadda hada-hada ta kaya ne kafin aka yanke shawarar sabon farashin man fetur.

Sanarar ta shawarci ‘dillalan man fetur da suyi amfani da sabuwar dokar da hukumar ta fitar.

A ranar 31 ga watan Mayun 2020 ne hukumar ta ba da sanarwar da cewa farashin man fetur ya karu daga naira 121.50 zuwa 123.50 a kan kowacce lita.

Rahotanni sun ce hauhawar farashin a watan Yuli ya zo ne sakamakon karin farashin danyen man da aka samu a kasuwar duniya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!