Connect with us

Labarai

Farashin Fetur na iya kaiwa Naira 2,000 idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba- PETROAN

Published

on

Kungiyar masu gidajen sayar da mai ta kasa PETROAN, ta yi gargadin cewa farashin Man  fetur na iya kaiwa kusan Naira 2,000 a kan kowace lita a nan gaba kadan , yayin da dizal zai iya tashi zuwa Naira 3,000, idan rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

 

Shugaban kungiyar na kasa, Billy Gillis-Harry, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a yayin wani taro a Jami’ar Ignatius Ajuru da ke birbin Fatakwal.

 

A cewar sa, tashin farashin mai a duniya da rikicin da ke kara tsananta tsakanin kasashen Israel, Iran, da kuma Amurka na iya jefa kasuwar makamashi cikin rudani, lamarin da zai iya janyo karin tsadar mai a kasar nan da sauran kasashen duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!