Kasuwanci
Farashin gas na girki ya tashi a Najeriya – NBS
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce farashin gas na girki ya tashi a watan jiya na Fabrairu.
A cewar hukumar ta NBS tukunyar gas mai nauyin kilogram biyar ya karu daga naira dubu daya da dari tara da arba’in da tara da kwabo biyu a watan Janairu zuwa naira dubu biyu da goma sha takwas da kwabo casa’in da daya.
Hakan na cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta wallafa a shafinta na website ne kan farashin gas na girkin a watan Fabrairu.
Hukumar kididdiga ta kasar ta kuma ce a wasu jihohin farashin ya karu fiye da haka, inda a jihar Bauchi ake dura tukunya mai nauyin kilogram biyar akan naira dubu biyu da dari hudu da tamanin da bakwai da kwabo arba’in da shida.
Sai kuma jihar Adamawa da aka rika durin akan dubu biyu da dari uku da casa’in da shida da kwabo casa’in da tara, yayin da jihar Borno ya kai naira dubu biyu da dari uku da casa’in da shida da kwabo ashirin da biyu.
You must be logged in to post a comment Login