Labarai
Farfesa Jega ya nemi gwamnatin tarayya data inganta rayuwar talaka
Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Attahiru Muhammad Jega, yaja hankalin gwamnatin tarayya da na jihohin kasar nan da su yi gaggawar samarwa da al’ummar kasar nan rayuwar mai kyau ta yadda za a magance irin halin kunci da kashe-kashe da garkuwa da mutane da al’ummar kasar nan ke fusanta.
Farfesa Attahiru Muhammad Jega na bayyana hakan ne a yayin taron shekara da gidauniyyar bunkasa rayuwar al’umma da samar da shugabanci na gari da inganta Ilimi ta Hudaibiyya ta shirya yau a dakin taro na kwalejin ilimin addinin musulinci ta Aminu Kano Legal.
Jega ya kuma ce akwai abubuwan da gwamnatin tarayya za ta iya gabatarwa cikin yan shekaru kalilan da a za a iya magance matsalolin da al’ummar kasar nan ke ciki.
Da yake jawabi yayin taron shugaban gidauniyyar Farfesa Muhammad Musa Borodo Jibril, ya ce sun shirya taron dan duba irin cigaban da kasar nan ta samu cikin shekaru hamsin da tara da kuma matsalolin da ta fuskanta dan samar da hanyoyin gyara.
Wasu daga cikin mutanan da suka halarci taron sun bayyana muhimmancin shirya taro inda suka yi kira ga gwamnatocin kasar nan da su samar da wata hanya da za ta ragewa ‘yan kasar nan radadin da suke fuskanta.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan da kuma dalibai da suka fito daga jami’oi da kwalejojin ilimi na jihar Kano.