Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fargabar tsaro: baƙin fuska na ci gaba da shigowa Kano

Published

on

Masanin tsaro a jamiar Yusuf Maitama Sule a nan Kano ya ce, jihar na cikin barazanar tsaro sakamakon yadda ake samun bakin fuska a cikin a yanzu.

Malam Auwal Bala Durumin Iya ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.

“Jihohin da suke fatattakar yar tada kayar baya, suna samun saukin matsalar tsaro, amma kuma yan ta’addan sun bazama zuwa wasu jihohin” in ji Durumin Iya.

Malam Auwal ya ce idan har ana son a magance matsalar yan bindiga a jihar nan, to kuwa dole ne sai an toshe duk wata hanyar da ake ganin za su iya biyowa domin shigowa.

Ya ce akwai babban kalubalen da ke shirin shigowa jihar Kano matukar ba’a magance c gaggawa ba, inda ya shawarci hukumomi su samar da dabaru don gujewa fuskantar matsala.

Durumin iya ya bayyana rufe iyakokin kano da jihar jigawa da katsina da ma Zamfara su ne kadai mafitar da jihar za ta zamu daga wadancan bata garin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!