Labarai
Faruk Lawan ya fara zaman gidan gyaran hali
Jami’an tsaro sun garzaya da tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono Faruk Lawan, zuwa gidan yarin Kuje da ke birnin tarayya Abuja.
Wannan da ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin shekaru bakwai.
Tun farko dai kotun ta kama Faruk Lawan da laifin karɓar na goron dala dubu ɗari biyar a wajen fitaccen attajirin nan, Femi Otedola.
Mai shari’a Angela Otaluka ta kotun birnin tarayya da ke unguwar Apo, yayin shari’ar, ta ce, ta kama Faruk Lawan da laifuka a dukkannin zarge-zarge uku da aka yi masa.
Rahotanni sun ce, bayan kammala zaman kotun ne sai jami’an tsaro suka tasa keyar tsohon ɗan majalisar zuwa gidan yarin na Kuje.
You must be logged in to post a comment Login