Labarai
Femi Falana ya zargi shugaba Trump da yin kalamai marasa tushe kan Najeriya

Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana mai shaidar ƙwarewa a fannin aikin lauya ta SAN, ya zargi shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, da yin kalaman da basu da tushe kan batun
kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista a kasar nan.
Falana ya bayyana cewa kalaman Trump ba su da tushe, yana mai zargin shugaban da nuna kyama da wariya ga ƙasashen Afirka, musamman Najeriya.
Ya ce irin waɗannan kalamai na iya haifar da rudani da kuma gurbata sunan ƙasar a idon duniya, inda ya bukaci Amurka ta guji yin siyasa da al’amuran addini na Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login