Labarai
Fifita muradan al’umma ga shugabanni zai sauya makomar Africa – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya buƙaci shugabannin ƙasashen Afirka su rika fifita muradun jama’a sama da son zuciyarsu domin tabbatar da ci gaban nahiyar.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 89 da haihuwarsa da Olusegun Obasanjo Leadership Institute ta shirya a Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke birnin Abeokuta, inda ya ce makomar Afirka tana hannun shugabanni masu ƙarfafa hukumomi.
Ya kuma jaddada cewa babban ƙalubalen Afirka ba rashin albarkatu ba ne, sai dai ƙarancin shugabanci nagari, tare da kira ga matasa masu koyon shugabanci da su ɗauki horon da suke samu a matsayin kira zuwa hidimar jama’a.
You must be logged in to post a comment Login