Labarai
Fiye da mutane 40 sun rasu sakamakon zaftarewar kasa da mamakon ruwa a Kenya

Zaftarewar kasa sakamakon kwanakin da aka shafe ana mamakon ruwa a Kenya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da arba’in.
Wakiliyar BBC ta ce a cewar ma’aikatar Ilimi, mutum 11 daga cikin wadanda suka mutu yara ne ƴan makaranta a yankunan da ke cike da tsaunuka da ke kan iyakar kasar da Uganda.
Masu aikin ceto daga kasashen biyu na ci gaba da neman gwamman mutanen da su ka bace.
Hukumomi na gargadin za a ci gaba da samun zaftarewar kasar, kuma an nemi wandanda ke yankunan su fice zuwa wuraren da ke kan tudu.
You must be logged in to post a comment Login