Labarai
Fiye da mutum miliyan 8 ne suka yi rijistar zaɓe ta Internet- INEC

Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC, ta bayyana cewa fiye da ƴan Najeriya miliyan takwas ne suka kammala rajistar zaɓe a matakin farko ta intanet, yayin da ake ci gaba da gudanar da rajistar masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasa.
Hukumar ta INEC ta cikin wani rahoto da ta fitar a birnin tarayya Abuja, ta ce, baya ga waɗanda suka yi rajistar a matakin farko, akwai kuma mutane miliyan ɗaya da dubu bakwai da suka kammala cikakkiyar rajistar.
Bisa ga ƙididdigar mako na tara dai jihar Imo ce ta fi yawan masu rajista da mutane dubu takwas da dari biyu da sittin da shida da ɗari takwas da hamsin, wanda ke daidai da kashi 10.32 cikin dari. Sai Jihar Legas mai dubun shida da ɗari huɗu da sittin da ɗaya da dari shida da goma sha tara watau kimanin kashi 7.56 sai Jihar Yobe wadda ta fi ƙarancin masu rajista da mutum dubun biyu da ɗari bakwai da goma sha huɗu, watau kashi 0.03.
Haka kuma, an dakatar da rajistar a Jihar Anambra, bisa tanadin sashe na tara sakin layi na shida na Dokar Zaɓe ta shekarar 2022, har sai bayan zaɓen gwamna da za a gudanar ranar takwas ga watan Nuwamba.
You must be logged in to post a comment Login