Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fursunoni 837 ne suka tsere a gidan gyaran hali na Oyo – NCS

Published

on

Hukumar kula da gidaje gyaran hali ta ƙasar nan ta ce fursunoni 837 da ke jiran shari’a sun tsere Abolongo lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai hari gidan.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Olanrewaju Anjorin, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Ibadan.

Anjorin ya ce, dukkanin fursunoni 837 da ke jiran shari’a a gidan sun tsare kuma maharan sun lalata dakunan da masu laifin ke ciki.

Sai dai ya ce, an samu nasarar kamo jimillar fursunoni 262 yayin da ake ci gaba da laluben 575.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kai wa gidan gyaran halin farmaki a ranar Juma’a da misalin karfe 9 da minti 30 na dare bayan da suka yi amfani da muggan makamai wajen shiga gidan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!